Marin dan majalisa: Majalisar jihar ta bukaci a cafko shugaban karamar hukuma

Marin dan majalisa: Majalisar jihar ta bukaci a cafko shugaban karamar hukuma

A ranar Laraba ne majalisar jihar Ebonyi ta bada umarnin gaggauta cafkowa tare da gurfanar da shugaban karamar hukumar Ohaukwu, Clement Odah, wanda ake zargi da cin mutuncin wani dan majalisar mai suna Chinedu Onah. Onah yana wakiltar Ohaukwu ta kudu ne a majalisar jihar.

An zargi cin mutuncin ya faru ne a dakin kwamitin majalisar jiha dake katafaren ginin majlisar a Nkaliki. An gano cewa, Odah ya fusata sakamakon zargin rashin amincewa da wasu mutane hudu da ya zaba don a sanya su a wata kwamiti, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito cewa, Odah ya kutsa dakin kwamitin a yayin da wasu ‘yan majalisar ke tattaunawa a kan ma’aikatu, bangarori da wasu cibiyoyin gwamnati a jihar a kan gabatar da kasafin kudi ga gwamna, inda ya waska wa dan majalisar kyakkyawan mari.

A yayin mayar da martani a kan lamarin, mataimakin bulaliyar majalisar, Benjamin Ezekomama, ya bayyana bangarensa na labarin kamar haka: “Lamarin ya faru ne a yayin da shugaban karamar hukumar yaci karo da dan majalisar. Bayan Dan majalisar ya gaishesa a wajen dakin sai yaki amsawa. Shigowar dan majalisar ke da wuya, shugaban karamar hukumar ya biyo bayansa yana tuhumarsa da cire mutanen da ya zaba don a nadasu a kwamitin."

"A take dan majalisar ya sanar dashi cewa, ba shi ya kawosa majalisa ba, mutane ne suka zabesa. A take kuwa shugaban karamar hukumar ya sakar masa mari a fuska, duk kuwa a gabanmu ne. Abun kunya!” ya kara da cewa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hakimin Birnin Gwari

A bangaren dan majalisar, ya tabbatar da abinda ya faru sannan ya zargi shugaban karamar hukumar da ci masa mutunci a gaban abokan aikinsa. Ya ce bashi da hannu ko masaniya wajen hana nada wasu wadanda shugaban karamar hukumar ya kawo.A takaice, shi ba mazabar dan majalisar yake wakilta ba.

Ya kara da cewa, idan a misali yayi hakan, ai aikinsa yake yi tunda ba hurumin shugaban karamar hukumar bane.

A bangaren shugaban karamar hukumar kuwa, ya musanta aukuwar lamarin, amma ya ce sun dan samu hargitsi da hayaniya, wacce mutane suka shiga suka sasanta su. Amma shi fa bai san da zancen mari ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel