Najeriya ta bude gidajen yari 32 da Boko Haram suka rufe

Najeriya ta bude gidajen yari 32 da Boko Haram suka rufe

- An bude gidajen yari 32 da aka rufe a yankin arewa maso gabas sakamakon hare - haren Boko Haram

- Kakakin hukumar kula da gidajen yari na kasa, Mista Francis Enobore, shine ya sanar da hakan ranar Laraba

- Gwamnatin tarayya ta amince da gina sabbin gidajen yari masu daukan mutane 3000 a kowanne yanki na kasa

Hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa (NCoS) ta sake bude wasu gidajen yari 32 da mayakan kungiyar Boko Haram suka rufe a yankin arewa maso gabas.

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Francis Enobore, ya fitar ranar Laraba a Abuja.

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, Mista Enobore ya bayyana hakan ne yayin ziyartar gani da ido a wani gidan yari dake Dukpa.

Najeriya ta bude gidajen yari 32 da Boko Haram suka rufe

Gidajen yari
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa an rufe gidajen yarin ne biyo bayan yawaitar hare - haren da mayakan kungiyar Boko Haram ke kai wa, inda suke sakin fursunoni tare da saka musu wuta.

DUBA WANNAN: Mata ta mutu wajen haihuwa bayan fasto ya ce haramun ne yin tiyata

"An bude jimillar gidajen yari 32 da aka rufe su a baya saboda harin da mayakan kungiyar Boko Haram suke kai wa," a cewar Mista Enobore.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da gina sabbin gidajen yari masu daukan mutane 3000 a kowanne yanki na kasa, inda yanzu haka an kusa kammala wacce ake gina wa a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel