Dalilin da yasa muka fasa tayar motar da aka dauko mai nakuda - FRSC

Dalilin da yasa muka fasa tayar motar da aka dauko mai nakuda - FRSC

Hukumar kiyaye hadurran kan titi ta tarayya, FRSC ta yi bayanin dalilin da yasa jami’anta suka fasa tayar motar da aka dauko mace mai nakuda a Fatakwal, jihar Ribas.

Idan zamu tuna, wani ma’abocin amfanin da kafar sada zumuntar zamani ta twitter ya zargi wasu jami’an hukumar da fasa tayar motar ‘yar uwar shi da ta dauko mata mai nakuda za ta kai ta asibiti.

Amma kuma, mai magana da yawun hukumar, Bisi Kazeem, a wata takaradar da ya bayyana ga manema labarai a ranar Lahadi a garin Abuja, ya ce an gayyaci mai tuka motar don binciken farko kuma daga bisani ga abubuwan da suka bankado:

“Da farko dai, wacce ke da cikin na zaune ne a kujerar gaba ta motar kuma ba ta sanya damarar da ke kujerar ba a lokacin da aka kama su kuma ko bayan da jami’an suka bukace ta da ta yi hakan.

Dalilin da yasa muka fasa tayar motarda aka dauko mai nakuda - FRSC
Dalilin da yasa muka fasa tayar motarda aka dauko mai nakuda - FRSC
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Mata ta mutu wajen haihuwa bayan fasto ya ce haramun ne yin tiyata

“Na biyu kuwa, wacce ake zargin na nakuda kuma za a kai ta asibiti duk ba haka bane. Kawai dai matar da ke tukin ta taimaka mata ne ta rage mata hanya.

“Na uku kuwa, matukiyar motar ba ta san wacece mai juna biyun ba don daukarta tayi a kan hanya don taimako.

“Na karshe kuwa, ba fasa tayar motar jami’an suka yi ba. Kawai shugaban kungiyar ya hana direbar motar tafiya ne,” yace.

Kazeem ya ce kungiyar binciken lamarin da shugaban ya kafa na samun tattaunawa da direbar don jin wacece mai nakudar don a shawo kan matsalar a saukake.

Ya jinjinawa masu amfani da kafafen sada zumuntar zamani a kan yadda suka yada matsalar har ta kai ga shugaban hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel