Sunaye: APC ta kafa kwamitin sulhu mai mutane 10 a karkashin Lawan

Sunaye: APC ta kafa kwamitin sulhu mai mutane 10 a karkashin Lawan

Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ta kafa kwamitin sulhu da kuma tuntuba domin sasanta rigingimun cikin gida da jam'iyyar ke fama da su a matakin tarayya da kuma wasu jihohi.

A wata sanar wa mai dauke sa sa hannun sakataren yada labaranta na kasa, Malam Issa Lanre Onilu, APC ta ce ta yanke shawarar kafa kwamitin ne bayan tuntuba mai zurfi.

A cewar sanarwar da APC ta wallafa a shafinta na Tuwita, jam'iyyar ta ce kafa kwamitin ya biyo bayan amincewar kwamitin zartar wa na kasa (NEC) a taron da suka gudanar ranar 22 ga watan Nuwamba.

Shugaban majalisae dattijai, Sanata Ahmed Lawan, shine zai jagoranci kwamitin yayin da tsohon shugaban jamiyyar APC na wucin gadi, Cif Bisi Akande, zai masa mataimaki.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, tsohon gwamna jihar Nasarawa, Umar Tanko Almakura, Sanata Kashim Shettima (tsohon gwamnan jihar Borno), ministan muhalli, Sharon Ikeazor da Alh. Nasiru Aliko Koki.

DUBA WANNAN: Wata jihar ta zabge ma'aikatunta zuwa 16

Ragowar sun hada da Sanata Khairat Gwadabe-Abdulrazak; Sanata Binta Garba da Seanata John Enoh a matsayin sakatare.

APC ta ce ta bawa kwamitin iko da karfin sulhunta rigingimun da jam'iyyar ke fama da su a kowanne mataki tare da warware rashin jituwar da ta fito fili a tsakanin wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar.

Sanarwar ta kara da cewa za a sanar da mambobin kwamitin ranar da za a rantsar da su domin su fara aikin da aka dora musu nauyinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel