Jerin Gwamnoni 8 da kotun koli ta baiwa nasara yau

Jerin Gwamnoni 8 da kotun koli ta baiwa nasara yau

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar gwamnonin jihohin takwas a zaben da aka gudanar ranar Laraba, 9 ga watan Disamban 2019.

Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen gwamnonin da yadda alkalan suka yanke hukuncinsu:

1. Dapo Abiodun (Ogun)

A jihar Ogun, jam'iyyar Allied Peoples Movement APM da dan takararta, AbdulKabir Akinlade, sun kai gwamnan jihar, Dapo Abiodun, kotu kan rashin amincewa da sakamakon zaben jihar.

A karshe, Kwamitin alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Mary Odili, sun yi ittifakin watsi da kararrakin jam'iyyar APM.

2. Udom Emmanuel (Akwa Ibom)

A Akwa Ibom, kotun ta yi watsi da karar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), da dan takararta, Nsima Ekere, inda mai shari'ar, Mary Odili, tace babu hujjoji masu tabbatar da zarge-zargen da sukayi.

3. Bello Masari (Katsina)

An tabbatar da Masari matsayin gwamnan jihar, Alkali Inyang Okoro ya yi watsi da karar Yakubu Lado da PDP inda suka bukaci tsige gwamnan kan zargin cewa takardun bogi ya gabatarwa hukumar INEC.

4. Abdullahi Sule (Nasarawa)

Bayan nasarorin da ya samu a kotu zabe da daukaka kara, kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar, Abdullahi Sule, kuma tayi watsi da karar jam'iyyar PDP da David Ombugadu.

5. David Umahi (Ebonyi)

A Ebonyi, Mai shari'a, Amina Adamu-Augie ta yi watsi da karar jam'iyyar Peoples Democratic Movement (PDM) da dan takararta Ajah Agha, kan cewa hukumar INEC ta zabge sunan jam'iyyar a takardar kuri'ar da akayi amfani da su ranar zabe.

6. Babajide Sanwo-Olu (Lagos)

Jam'iyyar Labour Party LP da dantakarta, Ifagbemi Awamaridi da kuma jam'iyyar Alliance for Democracy AD da dan takararta, Owolabi Salis, ne suka shigar da kara kan gwamnan jihar Legas, Jide Sanwoolu.

A karshe, Kwamitin alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Paul Galinje, sun yi ittifakin watsi da kararrakin jam'iyyar AD da LP.

7. Seyi Makinde

Kotun ta yanke hukunci ne a karar da Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya daukaka kan nasarar Seyi Makinde a zaben .

8. Nasir el-Rufai (Kaduna)

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka suka shigar da kara gaban kotun domin kalubalantar hukuncin nasarar El-Rufai a zaben gwamnan jihar da INEC ta sanar.

Kwamitin Alkalan bakwai sun yi watsi da karar gaba dayanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel