Tulin bashin da Shugaba Buhari ya ke karbowa Najeriya abin tsoro ne Inji Atiku

Tulin bashin da Shugaba Buhari ya ke karbowa Najeriya abin tsoro ne Inji Atiku

A Ranar 17 ga Disamban 2019, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi gargadi a game da bashin da gwamnatin Najeriya ta ke karbowa wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Alhaji Atiku Abubakar wanda ya yi takarar shugaban kasa a bana ya bayyana cewa bashin da Najeriya ta karbo daga kasar waje shekaru 30 na baya, shi ne abin da aka ci a shekaru ukun nan.

Atiku Abubakar ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Facebook ya na cewa: “Lamarin abin tsoro ne, ba wai duba da adadin kudin ba, ganin yadda ba a taba cin bashin irin wadannan kudi ba.

‘Dan adawar ya koka da yadda Najeriya ta zama Hedikwatar talaucin Duniya da kuma matattarar inda ake fama da yaran da ba su zuwa makaranta. “Ya kamata a tambayi ina ake kai kudin.”

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta zuba asarar sama da Biliyan 100 a bana

“Ganin Najeriya ta ware Naira tiriliyan 2.7 wajen biyan bashi (a bana), wanda ya haura Naira tiriliyan 2.4 da za a kashe wajen gina abubuwan more rayuwa ya nuna aron kudinmu ya yi yawa.”

“Bayan batar da rabin kudin da mu ke samu a wajen biyan bashi, wannan gwamnati ta na neman sake karbar bashin Dala biliyan 29.9.” Tun kwanaki IMF ta fara jan-kunnen a kan bashin kasar.

“Ni da Shugaba Olusegun Obasanjo mu ka biya bashin da ke kan kasar nan, ba za mu zura idanu mu na kallon wasu da ke neman girbi inda ba su yi shuka ba, su sake jefa Najeriya cikin bauta.”

“Dole Matasanmu su gaji wani abin, ba tulin bashi da wasu Mayunwata su ka taro ba. Wannan ya sa na yi kira ga Majalisa ta nuna kishin kasa, ta canza matsayarta game amincewa aron kudin.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel