Tababa a kan sabbin masarautu: Ganduje ya caccaki dattijan jihar Kano, ya ce basu san me jiha ke ciki ba

Tababa a kan sabbin masarautu: Ganduje ya caccaki dattijan jihar Kano, ya ce basu san me jiha ke ciki ba

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kano, Dakt Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki kungiyar dattijan jihar, inda ya kira su da 'yan ta fadi gasassa da basu san gaskiyar abubuwan da ke faruwa ba.

A kwanakin baya ne kungiyar dattijan jihar Kano a karkashin jagorancin tsohon dan takarar shugaban kasa, Bashir Tofa, ta soki kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano. Kazalika, kungiyar ta maka gwamnatin Ganduje a kotu a kan sabbin masarautun tare da bayyana cewa kirkirar sabbin masarautun ya saba da abin da jama'ar Kano ke so.

Da yake mayar da martani yayin zaman majalisar zartar wa ta jihar Kano a ranar Laraba, ganduje ya kare gwamnatinsa a kan kirkirar masarautun tare da bayyana cewa zai tabbatar da cewa duk dokokin da aka kirkira a kan sabbin masarautun sun fara aiki gadan-gadan.

Kazalika, yayin zaman majakisarGanduje ya taya manyan jami'an gwamnatinsa murnar nasarar da suka samu a kotu a kan kirkirar sabbin masarautun.

Tababa a kan sabbin masarautu: Ganduje ya caccaki dattijan jihar Kano, ya ce basu san me jiha ke ciki ba

Ganduje
Source: Twitter

A cikin jawabin kakakinsa, Abba Anwar, ya fitar a ranar Laraba bayan kammala zaman majalisar zartarwar, Ganduje ya bayyana cewa kirkirar sabbin masarautun zai kawo cigaba a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Bauchi: Kotu ta zartar da hukunci a kan matashin da ya kashe mahaifinsa a Masallaci

Ganduje ya ce tuni ya bayar da takardun tabbatar wa ga sabbin sarakunan yanka hudu da ya kirkira tare da bayyana cewa yanzu gwamnati zata mayar da hankali ne wajen inganta aiyukan sabbin masarautun tare da cigaba da kaddamar da sauran sabbin dokokin masarautun da majalisa ta amince da su.

A cewarsa, dattijan jihar Kano dake korafi a kan sabbin masarautun basu san abubuwan da ke faruwa ba a zahiri saboda 'yan tayi dadi ne kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel