Rikin fili: Yan daba sun yi wa basarake mugun duka, sun bar shi rai hannun Allah

Rikin fili: Yan daba sun yi wa basarake mugun duka, sun bar shi rai hannun Allah

Mai martaba Godwin Aigbe na yankin Ukhiri da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha ya fada doguwar suma bayan bakin dukan da wasu ‘yan daba suka yi masa.

An gano cewa, mai martaba Aigbe na karbar taimakon masana kiwon lafiya a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda tsaro.

An gano cewa, ‘yan daba sun hari fadarsa ne a wani hari da ake zaton na mayar da martani ne, inda suka ji masa miyagun ciwuka, kamar jaridar The Nation ta ruwaito.

Ganau ba jiyau ba sun ce, ‘yan daban sun harbeshi bayan nan kuma sun sossokesa a wurare daban-daban kuma sun ji masa ciwuka. ‘Yan daban sun lalata motoci biyar a cikin gidansa.

An gano cewa, mai martaba Aigbe yana da wata matsala da yankin Ulegun a kan wani yankin fili mai girman hekta 222. Dukkan yankunan sun kasance a cikin fada a kan filin tun a 1975.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Sakamakon zabuka 10 da suka ba 'yan Najeriya mamaki

Kanin wanda aka raunata din Enogie Kingsley Aigbe, yayi kira ga jami’an tsaro da su bincika a kan harin da aka kaiwa dan uwansa. Kingsley ya ce, an kirasa a daren Litinin cewa ya hanzarto don an hari dan uwansa.

Osayande Okhuarobo, wani mutum dan yankin ne, ya bayyana cewa sun cikin fadar ne lokacin da ‘yan daban suka kawo hari. Mutanen da ke gudu don tserar da rayuwarsu sunce, maharan sun zo ne daga kauyen dake da makwaftaka dasu.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce barkonon tsohuwa aka fara watsa musu, lamarin da yasa suka yi tunanin cewa ko fadar ce aka bankawa wuta. Ya ce, Enogie ya tsere amma sai ‘yan daban suka bi shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ki bada wani rahoto a kan mutuwa ko rayuwar Enogie.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel