Za a biciki cocin kasar Ingila da ake saida jini domin a samu kudin dawainiya

Za a biciki cocin kasar Ingila da ake saida jini domin a samu kudin dawainiya

Wata hukuma a Birtaniya ta ce za ta binciki cocin SPAC Nation game da rade-radin da ake ji na cewa Fastoci su kan bukaci Masu ibada su ci bashi, su saida jininsu domin su bada gudumuwa.

Jama'a su kan saida jinanansu ga masu bukata domin su samu damar dawainiyar wannan coci da ya yi kaurin-suna wajen facaka da dukiya. Jaridar waje ta Daily Mail ta kawo wannan rahoto.

Wani asalin Mutumin Najeriya mai suna Tobi Adegboyega, shi ne Faston da ke kula da wannan Coci na SPAC da ke kasar Ingila. Yanzu hukuma za ta yi bincike a kan abubuwan da su ke faruwa.

Kwanaki mu ka ji labari cewa shugabannin wannan coci na SPAC Nation sun yi wa wadanda ba su bada gudumuwar aikin addini barazana har ta kai an nemi su je su san inda za su samu kudi.

KU KARANTA: 'Wasu 'Yan bindiga sun sace Basarake a Garin Birnin Gwari

Manyan cocin sun fadawa Mabiyansu, “Su je su yi roko, nemi aro ko su yi sata” domin su kawo kudin da za a rika tarawa coci. Wani daga cikin Jagororin wannan coci ya shiga gidan yari.

An taba daure Mariam Mbuka a kasashen Ingila, Beljika da Sifen, kuma ta na cikin manyan cocin. Haka zalika ana neman ta ruwa a jallo a kasar Italiya da zargin aikata wani mummunan laifi.

Kunbiya-kunbiyar da ake bugawa a wajen sha’anin wannan coci ya zama abin damuwa ga hukuma. Kakakin hukumar ya kuma koka da yadda ake bi wajen tarawa cocin gudumuwa.

Cocin ya fito ya yi jawabi ya na cewa. “Idan aka kama wani Fasto ya na matsawa mutane, su bada gudumuwa, za a kore shi nan-take, balle a fara maganar saida jini domin bada gudumuwa.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel