Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hakimin Birnin Gwari

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hakimin Birnin Gwari

Masu garkuwa da mutane sun sace hakimin Birnin Gwari Central, Yusuf Abubakar a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a ranar Laraba kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Dama da dai hanyar da ma garin na Birnin Gwari ba ki dayansa ya yi kaurin suna a kan sace mutane.

An sace Yusuf Abubakar, mai rike da sarautar Sarkin Kudin Birnin Gwari ne tare da wani mai sarautar gargajiya, Ibrahim Musa, Wakilin Makarantar Birnin Gwari.

Daily Nigerian ta gano cewa an sace su ne misalin karfe 12 na rana a Unguwar Yako.

Kawo yanzu dai rundunar 'yan sandan jihar ta ba ce komai a kan afkuwar lamarin ba.

DUBA WANNAN: Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

A wani rahoton, mun kawo muku cewa mai martaba Godwin Aigbe na yankin Ukhiri da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha ya fada doguwar suma bayan bakin dukan da wasu ‘yan daba suka yi masa.

An gano cewa, mai martaba Aigbe na karbar taimakon masana kiwon lafiya a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda tsaro.

An gano cewa, ‘yan daba sun hari fadarsa ne a wani hari da ake zaton na mayar da martani ne, inda suka ji masa miyagun ciwuka.

Ganau ba jiyau ba sun ce, ‘yan daban sun harbeshi bayan nan kuma sun sossokesa a wurare daban-daban kuma sun ji masa ciwuka. ‘Yan daban sun lalata motoci biyar a cikin gidansa.

An gano cewa, mai martaba Aigbe yana da wata matsala da yankin Ulegun a kan wani yankin fili mai girman hekta 222. Dukkan yankunan sun kasance a cikin fada a kan filin tun a 1975.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel