Gwamnonin APC 2 - Legas da Ogun - sun samu gagarumin nasara a kotun koli

Gwamnonin APC 2 - Legas da Ogun - sun samu gagarumin nasara a kotun koli

Kotun koli - kotun da ke da hukuncin karshe a Najeriya - ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihohin Legas da Ogun a ranar Laraba, 18 ga Disamba, 2019.

Kotun ta tabbatar da gwamnonin biyu matsayin wadanda suka lashe zaben gwamnan jihohin da ya gudana ranar Asabar, 9 ga watan Maris, 2019.

Dukkan gwamnonin yan jam'iyyar APC ne.

Jam'iyyar Labour Party LP da dantakarta, Ifagbemi Awamaridi da kuma jam'iyyar Alliance for Democracy AD da dan takararta, Owolabi Salis, ne suka shigar da kara kan gwamnan jihar Legas, Jide Sanwoolu.

A karshe, Kwamitin alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Paul Galinje, sun yi ittifakin watsi da kararrakin jam'iyyar AD da LP.

A jihar Ogun kuwa, jam'iyyar Allied Peoples Movement APM da dan takararta, AbdulKabir Akinlade, sun kai gwamnan jihar, Dapo Abiodun, kotu kan rashin amincewa da sakamakon zaben jihar.

A karshe, Kwamitin alkalan kotun kolin karkashin jagorancin Jastis Mary Odili, sun yi ittifakin watsi da kararrakin jam'iyyar APM.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel