Kotu ta yi watsi da bukatar kudin fansho na wani tsohon gwamna

Kotu ta yi watsi da bukatar kudin fansho na wani tsohon gwamna

Kotun masana’antu ta kasa dake Abuja a ranar Laraba, tayi watsi da karar tsohon gwamnan jihar Borno, Mohammed Goni, a kan bukatar fanshonsa. Goni ne gwamnan farar hula na farko a jihar Barno daga watan Oktoba 1979 zuwa Oktoba 1983.

Ya bayyana cewa, tunda ya bar kujerarsa, an biyasa fansho ne na shekaru hudu, daga 2014 zuwa yau. A don haka ne yake bukatar gwamnatin jihar da ta yi biyayya ga tanadin kundin tsarin mulkin jihar Barno da ya bukaci a bashi fansho duk wata har karshen rayuwarsa. Tsohon gwamnan ya bukaci kotun da ta umarci gwamnatin jihar da ta biya shi bashin fanshon da yake bin ta.

Jastis Edith Agbakoba a yayin yanke hukunci ta ce, dokar gwamnatin jihar Barno ta 2005 bata da hurumin sa a biya tsoffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho saboda sunyi mulki ne kafin samuwar kundin tsarin mulki na 1999.

A don haka ne Agbakoba ta yi watsi da karar saboda rashin tushe balle makama.

DUBA WANNAN: Ba yaki da rashawa Buhari yake ba - Ango Abdullahi

Kamar yadda lauyan mai kara ya bayyana, tsohon gwamnan na bukatar mataimaki a mataki na 10 na aiki, sabbin motoci biyu da direbobi biyu. Yana bukatar gida mai dakunan bacci shida a cikin jihar, biyan kudin ruwa da wutar lantarki, kudin magani na matarsa da yaransa da hutun kwanaki 30 a cikin Najeriya ko kasar ketare.

Lauya mai kare gwamnati, Bulus Adamu na ma’aikatar shari’a, ya ce, wanda ke karar bai dace da wadannan romon fanshon ba tunda ya yi mulki ne kafin kundin tsarin mulki na 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel