Wata jihar ta zabge ma'aikatunta zuwa 16

Wata jihar ta zabge ma'aikatunta zuwa 16

Gwamnatin jihar Kwara ta zabge ma'aikatun jihar daga 19 da ta gada daga tsohuwar gwamnatin zuwa 16 kacal. Kwamishinan aiyukan gona da habaka karkara, Harriet Afolabi-Oshatimehin, ta sanar da hakan a ranar Laraba yayin jawabi ga majalisar zartarwa ta jihar, a kan hade wasu ma'aikatu da kuma kirkirar wata daya da aka yi.

Anyi taron ne kafin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya mika kasafin kudi gaban majalisar.

Afolabi ta bayyana cewa, anyi hakan ne don rage yawan kudin da ake kashewa ne a jihar kuma don kara karfafa ingancin aiyuka ga mutanen jihar.

"A yau Laraba, ana taron majalisar zartarwa ta jihar nan ne don tattaunawa a kan kasafin kudin jihar na 2020. Majalisar ta aminta dashi kafin Gwaman jihar ya gabatar dashi gaban majalisar jihar ta Kwara.

"Abu na biyu da aka tattauna a kai shine gyara tare da hade wasu ma'aikatu da kuma kirkirar guda daya a jihar," Afolabi ta ce.

Ta ce, tsohuwar ma'aikatar al'adu da bude ido an hadeta da ma'aikatar yada labarai da sadarwa, inda suka koma ma'aikatar sadarwa. Ma'aikatar masana'antu da albarkatu an hadeta da masan'antar kasuwanci, inda suka koma masana'antar dogaro da kai.

DUBA WANNAN: Ganduje ya gwangwaje Sadiq Daba ta kyautar miliyan N1

Ta ce, tsohuwar ma'aikatar tsari da tattalin arziki an hadeta da ma'aikatar kudi, inda suka koma ma'aikatar kudi da tsari. Yayin da tsohuwar ma'aikatar gidaje da habaka birane suka koma cikin ma'aikatar aiyuka da sufuri.

Afolabi-Oshatimehin ta ce, majalisar ta amince da kirkirar sabuwar ma'aikatar aiyuka na musamman.

Ta kara da cewa, tsohuwar ma'aikatar muhalli da dazuzzuka ta koma ma'aikatar muhalli, yayin da ma'aikatar lamurran mata ta koma ma'aikatar walwala da cigaba.

Ta ce, ma'aikatun aiyukan gona da habaka karkara, shari'a, wutar lantarki, albarkatun kasa, ilimi da cigaban mutane, kananan hukumomi da lamurran sarautar gargajiya, wasanni da habaka matasa, lafiya da ilimin manyan makarantu, sune sabbin ma'aikatun da wannan gwamnatin ta amince dasu.

"Abinda muke kokarin yi shine tabbatar da an biya wa mutane bukatunsu. Muna so mu tabbatar da cewa, an inganta walwalar 'yan jihar Kwara. ta yaya zamuyi hakan? Majalisar ta amince da rage yawan kudin da masana'antun ke ci kuma mu yi amfani da kadan din da muke dasu yadda ya dace," in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel