Majalisa za ta yi bincike a game da rufe shagunan ‘Yan Najeriya a Ghana

Majalisa za ta yi bincike a game da rufe shagunan ‘Yan Najeriya a Ghana

Daily Trust ta rahoto cewa majalisar dattawan Najeriya ta bukaci ayi bincike game da rade-radin da ake yi na cewa an rufe shagunan ‘Yan Najeriya akalla 600 da su ke yin kasuwanci a Ghana.

Sanata Ifeanyi Ubah shi ne ya tado da maganar a gaban majalisar dattawan kasar a zaman da aka yi a makon nan. Ubah shi ne mai wakiltar yankin jihar Anambra a karkashin jam’iyyar YPP.

Ifeanyi Ubah ya fadawa ‘Yan majalisa cewa akwai bukatar a gudanar da bincike a kan zargin cin mutunci da rashin adalcin da aka yi wa ‘Yan kasuwan Najeriya da masu shago a kasar Ghana.

Sanata Ubah ya ce ya damu sosai, ganin Ghana da Najeriya su na cikin kungiyar ECOWAS. Akwai nauyi da ya rataya a kan ECOWAS domin ganin ‘Ya ‘yanta sun yi aiki ba tare da tsangawama ba.

KU KARANTA: Wani 'Dan Najeriya ya gamu da ajalinsa daga dawowa Najeriya

A shekarar 2010, bincike ya nuna cewa kashi 60% na kasuwancin da ake yi a Ghana, ya fito ne daga Najeriya, a cewar Ifeanyi Ubah. Bayan nan kuma sai aka fara kai wa ‘Yan Najeriyar hari.

‘Dan majalisar ya kara da cewa Ghana ta dauki matakan da za su fusata ‘Yan kasuwan Najeriya ta hanyar kawo dokar hukumar GIPC ta 865 wanda ta rage adadin hannun jarin ‘yan kasar waje.

A karkashin wannan doka, ‘Yan kasuwar da su ka zo Ghana daga kasar waje ba za su iya mallakar hannun jarin da ya haura $20, 000 ba. Wannan zai hana Baki yin kasuwanci da kyau.

Sanata Binos Yaroe da Isa Jibril sun tofa albarkacin bakinsu game da batun, su na masu kira ayi bincike. Ahmad Lawan ya nuna cewa dole ne gwamnati ta kare hakkin ‘Ya ‘yanta a ko ina

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel