Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar da Aminu Masari matsayin gwamnan jihar Katsina

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar da Aminu Masari matsayin gwamnan jihar Katsina

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, matsayin wanda ya lashe zaben jihar da ya gudana ranar 9 ga Maris, 2019.

Alkalin kotun koli, Jastis Inyang Okoro, ya yi watsi da karar da PDP da dan takararta suka shigar saboda rashin isasshen hujja.

A ranar 21 ga watan Satumba, Kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Katsina da tabbatar da nasarar Gwamna Aminu Bello Masari a matsayin hallastacen wanda ya lashe zaben gwamna.

Jam'iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta Yakubu Lado Danmarke sun kallubalanci nasarar Masari kan cewa bai cika ka'idojin yin takarar gwamnan ba kuma an tafka magudi yayin zaben.

KU KARANTA: Da Babangida bai yiwa Buhari juyin mulki ba, da Najeriya ta fi haka cigaba - Femi Adesina

Daily Trust ta ruwaito cewa an samu rabuwar kai tsakanin alkalan kotun uku inda Mai shari'a EB Omotoso da Mai shari'a Justice AI Ityonyiman suka tabbatar da nasarar Masari yayin da Mai shari'a Hadiza Ali Jos ba ta amince da hakan ba.

A yayin yanke hukuncin, Mai shari'a Ityonyiman ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujojjoji da za su gamsar da kotu kan zargin da ya ke yi hakan ya sa aka yi watsi da karar yayin da Mai shari'a Jos ta ke ganin PDP tana da hujja a kan cewa an tafka magudi yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel