Tuwo na mai na: Shugaba Buhari ya nada uwargidar minista Ngige mukamin babbar sakatariya

Tuwo na mai na: Shugaba Buhari ya nada uwargidar minista Ngige mukamin babbar sakatariya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin tarayya guda 9, daga cikinsu har da Evelyn Ngige, uwargidar ministan kwadago, kuma aminin Buhari, Chris Ngige.

Gidan talabijin ta Channels ta ruwaito sauran manyan sakatarorin da Buhari ya rantsar a ranar Laraba, 18 ga watan Disambar shekarar 2019 a fadar Aso Rock Villa sun hada da: Hassan Musa, Aliyu Ahmed, Olusola Idowu, David Andrew, Umar Tijjani, Nasir Gwarzo, Nebeolisa Anako da Tope Fashedemi.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 3 yan gida daya a Katsina

Tuwo na mai na: Shugaba Buhari ya nada uwargidar minista Ngige mukamin babbar sakatariya

Buhari ya nada uwargidar minista Ngige mukamin babbar sakatariya
Source: Facebook

Da yake gabatar da jawabi yayin rantsar dasu, shugaba Buhari ya yi kira ga sabbin manyan sakatarorin da kada su bari bukatar kashin kansu ko kuma wani san ransu ya danne bukatar aikinsu, sa’annan ya nemi da su kasance masu riko da gaskiya da rikon amana.

Shugaba Buhari ya rantsar da sakatarorin ne jim kadan kafin shiga taron majalisar zartarwa na mako mako da aka saba gudanarwa a fadar gwamnatin Najeriya, wanda ya kunshi kafatanin ministocin Najeriya da wasu manyan hadiman shugaban kasa.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan siyasar Najeriya, musamman masu burin tsayawa takara ko wacce iri a zaben shekarar 2023 dasu kada su kuskura su sanya shi cikin sabgar siyasarsu.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 17 ga watan Disamba yayin da yake tarbar manyan baki da suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock Villa domin taya shi murnar cika shekaru 77 a duniya.

Buhari ya nemi yan siyasa masu burin tsayawa takara a zaben 2023 da su kasance sun yi aiki tukuru wajen yakin neman zabe, domin kuwa a wannan karo ba zai sake bari a yi amfani da sunansa wajen tafka magudin zabe ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel