Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa coci wuta kan zargin Fasto ya birne yaro ciki (Bidiyo da hotuna)

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa coci wuta kan zargin Fasto ya birne yaro ciki (Bidiyo da hotuna)

Mutanen unguwa sun bankawa cocin Sotitobire Miracle Centre, dake Akure, birnin jihar Ondo wuta a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2019.

Zaku tuna cewa wani dan karamin yaro dan shekara daya da haihuwa, Eniola Kolawale, ya bata a cocin ranar 10 ga watan Nuwamba, 2019.

Labari ya yadu da safiyar yau cewa an ga yaron a cocin amma da aka isa wajen, sai aka samu cewa ba gaskiya bane.

Wani mai idon shaida wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce abinda ya basu mamaki shine yan sanda suna kokarin hana mutane shiga cocin inda suka bazama cin zarafin mutane, suna fitittikarsu daga cocin.

"Yace: Ana yada jita-jitan cewa an ga yaron a mimbarin cocin misalin karfe 6 na safe, sai na garzaya cocin."

"Da na isa wajen, sai muka fara tambaye-tambaye, amma daga karshe muka gani cewa jita-jita ne kawai ya yadu."

"Kawai sai yan sanda suka fara dukan mutane, har da yan jaridan da suka zo daukan rahoto."

"Fushin haka ya sa mutane suka bankawa cocin wuta." kuma an kashe dan sanda daya.

Yan sandan sun ci mutuncin dan jaridan Breeze FM, Eniola, Temitope Adedeji of Western Post na Ajuwon Tosin na SaharaReporters kuma sun kwace kayan aikinsu.

A makon da ya gabata, jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS sun damke faston cocin, Babatunde Alfa.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan siyasa, sarakunan gargajiya da masu fada a ji a jihar suna iyakan kokarinsu wajen ganin cewa an sakeshi.

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa coci wuta kan zargin Fasto ya birne yaro ciki (Bidiyo da hotuna)

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa coci wuta kan zargin Fasto ya birne yaro ciki (Bidiyo da hotuna)
Source: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel