Ajali in yayi kira: Dan Najeriyar da ya shekara 45 a kasar Amurka ya gamu da ajalinshi jim kadan da sanya kafar shi a Najeriya

Ajali in yayi kira: Dan Najeriyar da ya shekara 45 a kasar Amurka ya gamu da ajalinshi jim kadan da sanya kafar shi a Najeriya

- Wani kwararren akawu mai shekaru 72 wanda ya yi murabus ya rasa ranshi bayan wasu makasa sun far mishi

- Agbosasa ya dawo daga birnin New York bayan da yayi aikin shekaru 45 a can

- Dawowarshi Najeriya babu dadewa ne, wasu makasan haya suka harbeshi a gidanshi sannan suka kone gawarshi kurmus

Wani kwararren akawu mai shekaru 72 wanda yayi murabus, mai suna Mutiu Agbosasa anyi mishi kisan gilla a gidanshi da ke Ikorodu, jihar Legas.

An kashe mutumin ne a gidanshi bayan da ya dawo Najeriya daga Amurka inda yayi aikin shekaru 45. An gano cewa, mamacin ya yanke shawarar yin murabus ne don dawowa Najeriya bayan da ya shekara 45 a birnin New York yana aiki.

Ajali in yayi kira: Dan Najeriyar da ya shekara 45 a kasar Amurka ya gamu da ajalinshi jim kadan da sanya kafar shi a Najeriya

Ajali in yayi kira: Dan Najeriyar da ya shekara 45 a kasar Amurka ya gamu da ajalinshi jim kadan da sanya kafar shi a Najeriya
Source: Facebook

Kamar yadda rahoton ya bayyana, wasu makasan haya ne suka hallakashi a gidanshi dake Ikorodu bayan ya dawo daga wani taron da yayi da abokanshi a wata mashaya dake tsibirin Legas.

Wani ma'aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Babatunde Naheemdeen Ayodeji ne ya wallafa wannan labarin a shafinshi. Ya bayyana yadda mutumin ke da matukar gaskiya kuma ana mutunta shi a Amurka.

KU KARANTA: Zan fara shiga aji na koyar da darasi a makarantu - Shugaban karamar hukuma

Ya bayyana cewa, wani makusancin iyalan ne ya sanar da cewa an harbe Agbosasa kuma an kone gawarshi.

Matar Agbosasa ta je majami'a da daren ranar da abun ya faru. Mai gadin gidansu ne ya kirata a kan cewa kada ta dawo gida a lokacin don a kan idonshi abun ya faru.

An gano cewa, Agbosasa ya dawo Najeriya ne tare da matarshi amma ya bar yaranshi hudu a birnin New York.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel