Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar gwamnan PDP a jihar Oyo

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar gwamnan PDP a jihar Oyo

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, matsayin wanda ya lashe zaben jihar da ya gudana ranar 9 ga Maris, 2019.

Kotun wacce ta zauna yau Laraba, 18 ga watan Disamba, ta yi watsi da shari'ar kotun daukaka kara tayi a watan Nuwamba.

Za ku tuna cewa a ranar 11 ga Nuwamba, kotun daukaka kara da ke zama a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo ta soke zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar.

Kotun ta yanke hukunci ne a karar da Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya daukaka.

Kotun ta dage hukuncin kotun sauraron karar zabe wacce ta jaddada nasarar Makinde. Sai dai kuma, kotun ba ta kaddamar da Adelabu a matsayin wanda ya yi nasara ba.

Duk da umurnin kotun, gwamnan Seyi Makinde ya cigaba da kasancewa gwamna zuwa yanzu kotun koli ta yanke hukunci na karshe.

Seyi Makinde ya bada wani balli cikin tarihinsa cewa ya kwashe tsawon shekara 13 na rayuwarsa wajen siyar da biredi a bakin asibitin Adeoyo a Ibadan, kafin ya zama Gwamnan jihar Oyo.

A cewarsa, ya kaddamar da ilimi kyauta a jihar ne domin ganin cewa mazauna jihar sun amfana wajen samun ingantaccen ilimi. Gwamna Makinde ya kuma bukaci iyaye a jihar da su dauki karatun yaransu sama da komai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel