Da duminsa: Kotun koli ta tabbatar nasarar gwamnan Nasarawa, Sule

Da duminsa: Kotun koli ta tabbatar nasarar gwamnan Nasarawa, Sule

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, matsayin wanda ya lashe zaben jihar da ya gudana ranar 9 ga Maris, 2019.

Kotun ta tabbatar da matsayar kotu zabe da na daukaka kara da suka baiwa Injiniya Sule nasara.

Za ku tuna cewa kotun daukaka karar dake zamanta a Makurdi, jihar Benue ta tabbatar da Injiniya Abdullahi Sule na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zababben gwamnan jihar Nasarawa a ranar Talata, 12 ga Nuwamba, 2019.

KU DUBA: Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar gwamnan PDP a jihar Oyo

Kotun ta yi watsi da karar da jam'iyyar People Democratic Party (PDP) da dan takararta, Emmanuel David Ombugadu, suka shigar kan zaben 9 ga Maris.

Kotu ta kara da cewa ko shakka babu ta amince da hukuncin kotun zabe da ta yanke cewa lallai Abdullahi Sule ne ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel