Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar da El-Rufa'i matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar da El-Rufa'i matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, matsayin wanda ya lashe zaben jihar da ya gudana ranar 9 ga Maris, 2019.

Kotun daukaka kara reshen Kaduna a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da zaben Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a matsayin gwamnan jihar Kaduna a zaben gwamna da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka daukaka kara a gaban kotun, inda suke kalubalantar hukuncin kotun zabe, wacce ta kaddamar da El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zabe mai zaman kanta da fari ta kaddamar da El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Amma jam’iyyar PDP da dan takararta suka shigar da korafi gaban kotun zabe kan hujjar cewa anyi magudi sosai a zaben.

Sun bukaci kotun zaben da ta soke kuri’u 515,951, wanda suka yi ikirarin cewa an karawa APC ba bisa ka’ida bad a kuma kuri’u 124,210 da suka ce an karawa PDP, ta hanyar kuskure ko shigar da sakamakon sau biyu a takardar zabe wanda INEC ta yi.

A halin da ake ciki, kotun kolin ta tabbatar da hukuncin da kotun zaben da ta yanke sannan ta kaddamar da Gwamna Ahmad Nasir El-Rufai a matsayin ainahin zababben gwamnan jihar.

Ga dai cikakken sakamakon da hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar.

KAURA LG APC – 8, 342 PDP – 38, 764

MAKARFI LG APC – 34, 956 PDP – 22, 301

JABA LG APC – 6, 298 PDP – 22, 976

KUDAN APC – 28, 624 PDP – 22, 022

IKARA LG APC – 41, 969 PDP – 22, 553

KUBAU LG APC – 67, 182 PDP – 17, 074

KAJURU LG APC – 10, 229 PDP – 34, 658

GIWA LG APC – 51, 455 PDP – 19, 834

KAURU APC – 34, 844 PDP – 31, 928

KACHIA LG APC – 30, 812 PDP – 51,780

SOBA LG APC – 55, 046 PDP – 25, 440

ZANGON KATAF LG APC – 13, 448 PDP – 87, 546

SANGA LG APC – 20, 806 PDP – 21, 226

KADUNA TA AREWA APC – 97, 243 PDP – 27, 665

BIRNIN GWARI LG APC – 32, 292 PDP – 16, 901

CHIKUN LG APC – 24, 262 PDP – 86, 261

SABON GARI APC – 57, 655 PDP – 25, 519

LERE LG APC – 71, 056 PDP – 45, 215

JEMA’A LG APC – 21, 265 PDP – 63, 129

KAGARKO LG APC – 21, 982 PDP – 26, 643

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel