Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 3 yan gida daya a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 3 yan gida daya a Katsina

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kutsa kai gidan wani Malam Shamsuddeen Yusuf dake zaune a rukunin gidajen malamai na makarantar sakandarin kimiyya ta garin Dutsanma a kan babbar hanyar Dutsanma zuwa Kankara, jahar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun kaddamar da harin ne a daren Litinin inda suka tattara matarsa, Nana Bilkisu, kanwarsa Aisha Slaisu da kuma diyarsa mace Afnan Shamsu suka yi awon gaba dasu.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari jahar Adamawa, sun sace mutane 5, sun harbe Yansanda 4

Wasu majiyoyi dake kusa da iyalan sun bayyana cewa yan bindigan sun tuntubi Malam Shamsu, kuma sun nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 20 idan har ana so su sako matan uku da ransu ba tare da sun cutar dasu ba.

Da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar game da batun, sai Kaakakin rundunar, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace miyagun sun kai harin ne da misalin karfe 2:30 na dare.

A wani labari makamancin wannan daya faru duk a jahar Katsina, wani magidanci, Sanusi Lawal tare da matarsa sun fada hannun miyagu masu garkuwa da mutane a kauyen Dayi cikin karamar hukumar Malumfashi.

Shi dai Sanusi Lawal kanin dakacin kauyen Dayi ne, Alhaji Yahaya Lawal, kuma tuni yan bindigan sun tuntube danginsa suna neman kudin fansa naira miliyan 6 kafin su sako shi.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da sabon farmaki a karamar hukumar Ganye na jahar Adamawa inda suka yi awon gaba da mata masu shayawar guda biyu da kuma kananan yara guda uku.

Yan bindigan su dayawa sun kai harin ne da misalin karfe 2 na daren Talata, inda kai tsaye suka zarce gidan wani attajiri Alhaji Hussaini, a nan ne suka kwashe mata biyu da kananan yara uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel