Yan bindiga sun kai hari jahar Adamawa, sun sace mutane 5, sun harbe Yansanda 4

Yan bindiga sun kai hari jahar Adamawa, sun sace mutane 5, sun harbe Yansanda 4

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da sabon farmaki a karamar hukumar Ganye na jahar Adamawa inda suka yi awon gaba da mata masu shayawar guda biyu da kuma kananan yara guda uku.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan su dayawa sun kai harin ne da misalin karfe 2 na daren Talata, inda kai tsaye suka zarce gidan wani attajiri Alhaji Hussaini, a nan ne suka kwashe mata biyu da kananan yara uku.

KU KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a jami’ar Filato

Wani dan gidan ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa harbe harben bindiga ne ya tarwatsa mutane inda kowa ya yi ta kansa domin neam tsira, ya kara da cewa koda jami’an rundunar Yansanda suka isa gidan, sai aka shiga musayar wuta tsakaninsu da yan bindigan.

Sai dai yan bindigan sun fi karfin Yansandan, tunda har suka raunata Yansanda guda hudu daga cikinsu, sa’annan suka tsere da mutane biyar da suka sata daga gidan Alhaji Hussaini.

A nasa jawabin, kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace tuni sun kaddamar da bincike a kan lamarin domin lalubo inda yan bindigan suka tsere.

“Da tsakar daren Talata yan bindigan suka kai hari a gidan Hussaini AHmadu ake mazabar Wukari cikin garin Ganye inda suka yi awon gaba da matasan biyu da yaransa guda biyu, DPO tare da tawagarsa sun isa wurin cikin lokaci, amma sai yan bindigan suka yi musu kwantan bauna, anan aka yi ma musayar wuta har jami’anmu biyu suka samu rauni.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kungiyar daliban jami’ar jahar Filato, Ezekeil Lutei ya tabbatar da hari da wasu gungun yan bindiga suka kaddamar a jami’ar a ranar Talata, 17 ga watan Disamba, har ma suka yi ma wata daliba fyade.

Yan bindigan sun kai harin ne a jami’ar dake garin Bokkos kamar yadda shugaban daliban ya bayyana, ya kara da cewa sun yi ma dalibai da dama kwacen wayoyin salula da kudadensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel