Akalla Matasa miliyan 100 su ke fama da matsalar rashin abin yi - Ngige

Akalla Matasa miliyan 100 su ke fama da matsalar rashin abin yi - Ngige

Mun samu labari gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai Matasa akalla miliyan 100 a Najeriya da ba su da aiki mai-tsoka a Najeriya.

Gwamnatin kasar ta yi wannan bayani ne ta bakin Ministan kwadagon Najeriya, Dr. Chris Ngige, wanda ya shaidawa Duniya wannan a jiya.

Da yake jawabi a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja, a Ranar Talata, 17 ga Watan Disamba, 2019, ya fitar da wannan alkaluma.

“Mutanen Najeriya sun haura miliyan 200, wanda kuma kashi 60% na cikinsu Matasa ne da ke bukatar aikin yi a kasar.” Inji Chris Ngige.

KU KARANTA: Ana bukatar Malamai fiye da 270, 000 a Makarantun Najeriya

Abin takaicin dai shi ne mafi yawan Matasan ba su da abin yi kamar yadda Ministan ya shaida. “10% na Matasan ne kurum su ke da aikin kirki.”

“Babu wanda zai iya daukar wasunsu da dama aiki, yayin da wasu kuma ba su da aikin yi. Mu na kokarin ganin sun samu abin yi, su samu na kashewa.”

Ministan kwadagon ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na kokarin ganin yadda wadannan Matasa za su samu abin yi domin su more rayuwarsu.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Dr. Ngige ya yi wannan jawabi ne a wajen wani tarin tattaunawa da aka shirya game da hijira ana barin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel