Tabarbarewar tsaro: Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a jami’ar Filato

Tabarbarewar tsaro: Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a jami’ar Filato

Shugaban kungiyar daliban jami’ar jahar Filato, Ezekeil Lutei ya tabbatar da hari da wasu gungun yan bindiga suka kaddamar a jami’ar a ranar Talata, 17 ga watan Disamba, har ma suka yi ma wata daliba fyade.

Jaridar Punch ta ruwaito yan bindigan sun kai harin ne a jami’ar dake garin Bokkos kamar yadda shugaban daliban ya bayyana, ya kara da cewa sun yi ma dalibai da dama kwacen wayoyin salula da kudadensu.

KU KARANTA: Yaba kyauta tukwici: Dalibi ya raba ma tsofaffin Malamansa motocin alfarma a Daura

“Abin da ya faru ne shi ne an tsara wani shirin wasan kwaikwayo tsakanin daliban aji 2 da aji 4 a sashin koyar da wasan kwaikwayo na jami’ar, kwatsam da misalin karfe 10 na dare sai yan bindiga suka dira wurin, a nan ne suka yi ma wata daliba fyade, sa’annan guda ta samu rauni.

“Bugu da kari yan bindigan sun kwace wayoyin dalibai da dama, da kuma kudadensu, daga nan kuma suka tsere ba tare da mun san inda suka shiga ba. Ba wannan bane karo na farko da yan bindiga suke mana haka a makarantar nan, don haka akwai bukatar karfafa tsaro a jami’ar don kare rayukan dalibai da dukiyoyinsu.” Inji shi.

Daga karshe shugaban dalibai Lutei yace sun garzaya da dalibar da aka yi ma fyade zuwa asibiti mafi kusa domin samun kulawa, sa’annan sun kai rahoton lamarin ga hukumar jami’ar domin daukan matakin daya dace.

A wani labarin kuma, wata kotun majistri dake zamanta a garin Abakaliki na jahar Ebonyi ta bada umarnin garkame wata mata mai shekaru 40 a gidan gyara halinka biyo bayan tuhumar da ake mata na kashe mijinta.

Matar ta kashe mijinta, Nome Usulor ne ta hanyar caccaka masa wuka da kuma fasashshen kwalba a ranar 30 ga watan Nuwamba a unguwar Umoure-Oriuzor dake cikin karamar hukumar Ezza ta Arewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel