Ko a jikina zagina da 'yan soshiyal midiya ke yi - Rahama Sadau

Ko a jikina zagina da 'yan soshiyal midiya ke yi - Rahama Sadau

- Kyakyawar jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa ita ko a jikinta sukar da mutane ke mata

- Ta bayyana cewa, ko hijabi ta saka sai an samu masu magana a soshiyal midiya, a don haka ba a iyawa mutum

- Tace abun haushin shine yadda mutane ke dorawa kansu matsalolin wasu amma suna barin nasu ba tare da sun shawo kai ba

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana cewa ita ko a jikinta sukar da mutane ke yi mata a soshiyal midiya.

Ta ce, kowa da ra'ayinsa kuma ko me tayi sai an samu masu sukarta ko korafin ba daidai bane. Hakan yasa take komai nata kai tsaye.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ta yi da mujallar Fim.

Sanannen abu ne cewa Rahama Sadau na daya daga cikin 'yan Fim da suka yi kaurin suna a wajen jama'a.

A cikin kwanakin nan ne ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta kuma ta shirya babbar liyafa inda ta bude 'Sadau Homes'. Waje ne katafare da ya kunshi wajen cin abinci, kwalliya, gyaran jiki da wajen shan shisha.

Mutane da dama sunyi Alla-wadai da irin shigarta a ranar domin kuwa hannunta daya bude yake, hakazalika kafarta daya.

KU KARANTA: To fah: Yadda wata karuwa ta shiryar dani ta gyara mini rayuwata - Wani mutumi

Baya ga hakan, wajen shan Shisha din ya jawo cece-kuce daga jama'ar gari da suke ganin gurbata tarbiya take yi.

A yayin da mujallar Fim ta tambayeta a kan yadda take ji saboda irin yamadidin da ake ta mata, Sai Rahama ta ce, "Wallahi mutane ke jin surutun, ba ni ba. Idan mutane miliyan zasu yi magana, wallahi bana gani. Idan a yau hijabi na saka, nasan sai anyi magana. Don haka wallahi ban damu ba," a cewarta.

Kyakyawar jarumar ta bayyana cewa, surutu a soshiyal midiya baya karewa don haka ita bata damu ba. Ta ce abun bakin cikin shine yadda mutane ke bada muhimmanci a kan lamurran wasu daban amma suna manta wanda ke gabansu. Kowa yana da matsalarshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel