Gwamnatin Najeriya ta yi asarar N111b daga matatun danyen mai - NNPC

Gwamnatin Najeriya ta yi asarar N111b daga matatun danyen mai - NNPC

Matatun man gwamnatin tarayyar Najeriya uku, sun hadu sun buga asarar Naira biliyan 111.27 a cikin watanni tara. Rahoton da NNPC ya fitar ya nuna wannan mummunan ciniki da aka yi.

Kamar yadda rahoton NNPC ya nuna, matatun sun yi asarar wannan kudi ne daga farkon Junairun 2019 zuwa Satumba. A daidai wannan lokaci, kasar ta yi asarar biliyan 86.31 ne a bara.

Najeriya ce kasar Afrika da ke kan gaba wajen hako danyen mai, amma kasar ta dogara ne da kasashen waje wajen samun man fetur saboda rashin lafiyayyun matatu da za a tace man a gida.

Najeriya ta na da manyan matatun mai a Fatakwal, Warri da kuma Kaduna. Duk da labaran yunkurin gyara matatun kasar, har yanzu ana shigo da mai ne Najeriya daga kasashen waje.

Rahoton da kamfanin NNPC na Najeriya ta fitar ya nuna cewa ta yi asarar N8.362bn a cikin watan Junairu, sai N10.26bn a Fubrairu, kafin asarar ta tashi har zuwa N16.04bn a cikin Watan Maris.

KU KARANTA: Hyundai za su bude kamfanin motoci, su gyara matatun mai

NNPC ta yi asarar N11.44bn a Watan Afrilu, sai a cikin Mayu aka gamu da wata asarar ta N13.63bn. A watan Yuni abin ya cabe matuka, matatun sun jawowa kasar asarar N17.42bn.

Har ila yau, matatun sun rasa N13.84bn a Yuli da N13.21bn a Watan Agusta. A Watan Satumba, asarar ta takaita da N13.21bn. Kamfanin bai fitar da rahoton abin da ya auku daga Oktoba ba.

Matatar Kaduna da ba ta tace ko da gwangwanin danyen mai ba a bana ba, ta yi asarar biliyan 44.06. Matatar Warri ta tafka asarar Naira biliyan 33.88. An rasa biliyan 33.31 a matatar Fatakwal.

Idan matatun kasar su na aiki garau, za a iya samun tacaccen mai akalla ganga 445, 000 a duk rana. Ana sa ran cewa a shekara mai zuwa matatar da Dangote ya ke ginawa ta soma aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel