Kwamitin Majalisa ta na zargin bacewar N1.2b a hukumar jirgin kasa

Kwamitin Majalisa ta na zargin bacewar N1.2b a hukumar jirgin kasa

Mun samu labari cewa majalisar wakilan tarayya ta kuma gano cewa akwai yiwuwar bacewar wasu kudi a hukumar NRC mai kula da harkar jirgin kasa a Najeriya.

Shugaban kwamitin binciken kudin gwamnati, Hon. Wole Oke, ya jefi hukumar NRC da wannan zargi a zaman da majalisar ta yi a Ranar 17 ga Watan Disamba, 2019.

Honarabul Wole Oke, ya bayyana cewa NRC ta gaza kare kanta daga zargin bacewar Naira biliyan 1.2 daga cikin asusunta. Jaridar Daily Trust ta kawo wannan rahoto.

Kwamitin majalisar ba ta gamsu da bayanin da shugabannin NRC su ka yi masu ta bakin Misis O. Osunmade da Alhaji A. Niyi a game da zargin bacewar kudin ba.

Ofishin babban Akawun gwamnatin tarayya ya na zargin cewa akwai alamar tambaya game da kudin da hukumar NRC ta kasa ta batar a shekarar 2013 da 2014.

KU KARANTA: Matakin bizan Shugaban kasa ya dauka bai kwantawa Majalisa a rai ba

Kwamitin Majalisa ta na zargin bacewar N1.2b a hukumar jirgin kasa

Hon. Wole Oke ya ce Majalisa za ta binciki lamarin hukumar NRC
Source: Twitter

Oke ya nuna cewa martanin da hukumar kula da harkokin jirgin kasar ta bada a gaban kwamitinsa ta bakin O. Osunmade da kuma A. Niyi, sam bai gamsar da su ba.

Honarabul Oke mai wakiltar Mazabar Oriade/Obokun tun 2015 ya ce: “Dole mu sake duba lamarinsu da kyau domin gano gaskiya. Za mu kafa wani karamin kwamiti”

Wannan karamin kwamiti a karkashin kwamitin majalisar zai binciki zargin da ake yi wa hukumar, sannan ya gano gaskiyar ko wadannan kudi sun bace ko akasin haka.

A farkon makon nan kun ji cewa majalisar wakilan ta na zargin cewa Naira biliyan 14.8 sun bace daga hukumar kwastam mai yaki da fasa-kauri a daidai wannan lokaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel