Hyundai za su bude kamfanin motoci, su gyara matatun mai – CEO

Hyundai za su bude kamfanin motoci, su gyara matatun mai – CEO

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya za ta hada-kai da kamfanin Hyundai Engineering LTD na Duniya wajen bude wurin da za a rika kera motoci a kasar nan.

Bayan wannan kuma, kamfanin zai taimakawa Najeriya da ganin an babbako da matatun danyen mai na kasar. Wannan zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arziki da samar da aikin yi.

Shugaban Najeriyar ya bayyana wannan ne a fadar shugaban kasa, a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kamfanin Hyundai wanda su ka yi fice a sha’anin fasaha, Chang Hag Kim.

Chang Hag Kim da ‘Yan tawagarsa sun ziyarci shugaban na Najeriya ne a Ranar Talata, 17 ga Watan Disamba, 2019, a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto.

KU KARANTA: An rage yawan Keke - Napep da ke jihar Kano Inji KAROTA

Hyundai za su bude kamfanin motoci, su gyara matatun mai – CEO

Kamfanin Hyundai za su kafa wajen hada motoci a Najeriya
Source: Twitter

Shugaban kasar ya bayyana cewa Najeriya ta na kokarin ganin ta samu fetur da sauransu. “Burin shi ne Najeriya ta mallaki kayan mai nan da shekaru uku masu zuwa. Inji Shugaba Buhari.

Muhammadu Buhari ya ji dadin wannan shiri da kamfanin ya ke yi na kafa wajen kera motoci. Shugaban kasar ya ke cewa: “Za mu ba ku hadin-kai, mu ga wannan shiri na ku ya yi nasara”

Mista Hag Kim ya ce kamfaninsu mai ma’aikata fiye da 15, 000 zai bada irin na sa gudumuwar wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Kamfanin ya kware wajen gina matatar mai a Duniya.

“Mu na gina matatan mai a fadin Duniya. Mu ke da matatar da ke tace gangar mai 650, 000 a kasar Koriya ta Kudu. Mu na da matatu a Venezuela, Iraq da wasu kasashen.” Inji Hag Kim.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel