Ku daina tsaface-tsaface da shiga kungiyoyin asiri - Limamin coci ya shawarci 'yan siyasa

Ku daina tsaface-tsaface da shiga kungiyoyin asiri - Limamin coci ya shawarci 'yan siyasa

- Faston wata babbar majami'a da ke Enugu, Rabaran Ejike Mbaka ya ja kunnen 'yan siyasa

- Ya bukacesu da su fawwala lamurransu ga Ubangiji a kan shiga kungiyoyin asiri

- Ya tabbatar musu da cewa, mulki na hannu Ubangiji ba hannun kungiyoyin asiri ba

Faston wata babbar coci da ke Enugu, Rabaran Ejike Mbaka ya ja kunnen shuwagabannin siyasa da su guji kungiyoyin asiri.

Malamin ya bada wannan jan kunnen ne a ranar Lahadin da ta gabata.

Kamar yadda ya ce, wasu 'yan siyasar na shiga kungiyoyin asiri ne don samu kariya da kuma nasara a siyasarsu.

Ya ce: "Idan wasu daga cikinku na cikin wata kungiyar asiri, zai fi muku idan kuka fita kafin lokaci ya kure muku. Wadanda suke cikin kungiyar nan basu more kwanakinsu na karshe, basu bada kariya.

"Zasu iya muku alkawarin alfarma kala-kala, amma alfarma daga Ubangiji take zuwa. Toh kuma a wajenshi ake dogaro saboda shi ke bada mulki."

KU KARANTA: Tashin hankali: Yadda wasu mutane da ba'a san daga ina suke ba suka je wani kauye a garin Fatakwal suka yiwa mata sama da 1,200 fyade

"Kuna tunanin wannan rashin hankalin da kuke yi ne zai kaiku Inda kuke so? Toh ba gaskiya bane. Ubangiji zai iya daga ku ko kuma ya mayar daku baya." In ji shi.

Mbaka ya kara dora laifin halin matsin da 'yan kasa ke ciki a kan shuwagabanni. A maimakon inganta rayuwar mutane, sai waskar da dukiyar baitul mali sukeyi zuwa manyan aljihunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel