Tashin hankali: Yadda wasu mutane da ba'a san daga ina suke ba suka je wani kauye a garin Fatakwal suka yiwa mata sama da 1,200 fyade

Tashin hankali: Yadda wasu mutane da ba'a san daga ina suke ba suka je wani kauye a garin Fatakwal suka yiwa mata sama da 1,200 fyade

- Sarah budurwa ce mai shekaru 25, ta bayyana yadda wasu katti dauke da makamai suka yi mata fyade

- Ta bayyana yadda mazan suka rufe fuskarsu sannan suka kutso cikin gidansu da karfe 2 na tsakar dare

- Nauyin sanar da cin zarafin tare da yadda mutane zasu kalla Sarah ne yasa ta kasa sanar da ‘yan sanda

“Sun kutso cikin garinmu wajen karfe 2 na dare. Sun yi mana fyade. A lokacin da zasu tafi, sun tafi da wayoyinmu da kudinmu.”

Wadannan sune kalaman Sarah da ta kwatanta tashin hankalin da suka shiga a lokacin da da wasu maza biyu dauke da makamai suka kutsa gidansu da ke garin Fatakwal.

Gano su waye mazan ne ya zama wani abunda ya gagara saboda fuskokinsu duk rufe take.

A yayin jin nauyi tare da tunanin yadda mutane zasu kalleta, budurwar mai shekaru 25 ta ki sanar da kowa anyi mata fyade. Ko ‘yan sanda, ‘yan uwanta balle kuma kawayenta.

“A nan ba a maganar irin wadannan abubuwan,” Sarah ta ce.

Daga bisani, Sarah ta garzaya ga masana kiwon lafiya don su binciketa. A nan ne ta samu magunguna. Daga baya ne ta samu karfin sanar da masanin halayyar dan Adam halin da take ciki.

Daga yawan mutanen da cibiyar kiwon lafiyar ta samu korafinsu, a kalla majinyata 1,200 ne suka bukaci taimakon cibiyar kiwon lafiyar a kan matsalar fyade a garin Fatakwal din.

KU KARANTA: Mutanen da suka yi wakar 'Buhari Jirgin Yawo' sun azabtu a hannun wani dan siyasa

Garin Fatakwal na da manyan matsalolin da suka hada da tsananin fatara da rashin daidaituwa, wanda ya yi katutu a babban garin. Hakazalika, gari ne da kungiyoyin asiri suka yi dankam a ciki. Sun samu wajen zama ne a manyan makarantun da suke garin. Yawan kungiyoyin yasa ake samun fadace-fadace tsakaninsu.

Wadannan ‘yan kungiyoyin sukan kai samame, garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da sauran laifuka. Sau da yawa kuwa wadanda abun ya ritsa dasu, ballantana mata kan fuskanci matsalolin cin zarafi.

“A duk lokacin da ake samun fadace-fadacen ‘yan kungiyar asiri a yankin, mutane kan tarwatse kuma a hakan ‘yan fashi da makami ke samun damar shiga gidaje har su yi wa yara mata fyade,” cewar Christine Harrison.

Matar mai shekaru 42 ta kasance mai sintiri ne a titunan garin don mika lambar da za a kira a lokutan bukatar gaggawa, aikin da ta ke yi na shekaru biyu kenan.

“Aikina shine in zaburar da mata su tashi tsaye don kwatar ‘yancinsu,” ta ce. “A da, fyade bai yawaita ba a duniya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel