Rashin aminta da karin wa'adin mulki: Baku yi amfani da damarku ba - Atiku

Rashin aminta da karin wa'adin mulki: Baku yi amfani da damarku ba - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana rashin jin dadinsa ta yadda 'yan majalisa suka yi watsi da mayar da wa'adin mulkin shuwagabannin kasa da gwamnoni zuwa shekaru shida-shida.

Abubakar ya nuna rashin jin dadinsa a takardar da ya mika ga mai bashi shawara a kan yada labarai, Paul Ibe, a ranar Talata a Abuja yayin mayar da martani a kan bukatar da majalisar ta yi watsi da ita a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito.

Ya ce, ya sha mamakin yadda 'yan majalisar suka wurgar da jinjiri a cikin ruwan wanka a maimakon tarairayarsa.

Abubakar ya ce, idan aka yi duba da kalubalen da Najeriya ke fuskanta, ballantana magudin zabe da akeyi don kwace yancin mutane, wannan wa'adin mulkin zai kawo gyara a bangaren.

"Son zarcewa da masu mulki ke yi duk zai ragu. Ta haka ne kuma za a iya yin zaben na gaskiya da amana a kasar nan. Zai kuma sa masu mulkin su mayar da hankali wajen aiwatar da aiyukansu tare da cimma manufofinsu."

DUBA WANNAN: Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

Abubakar ya bayyana damuwarsa ta yadda masu mulki ke amfani da kujerarsu tare da kudin gwamnati wajen komawa mulki a karo na biyu ko ta wanne hali.

"Ban yarda da hikimar cewa, shekaru takwas ne zasu ba shuwagabanni damar sauke nauyin alkawarin da suka dauka wajen yakin neman zabe ba. Duk shugaban da ba nagari ba, ba zai iya yin komai ba koda kuwa an kara masa shekaru masu yawa," Abubakar ya jaddada.

Kamar yadda ya ce, ba dadewa a kujera bane, kaifin basirar aiki mai kyau daban ne. Ya ce son komawa mulki karo na biyu, ba kishin kasa bane. Son mulki ne kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel