Ba yaki da rashawa Buhari yake ba - Ango Abdullahi

Ba yaki da rashawa Buhari yake ba - Ango Abdullahi

Shugaban zauren dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi a ranar Talata ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba yaki da rashawa yake yi ba a kasar nan. Ya ce, "Kamata ya yi a ce yanzu gidan gyaran hali na cike dankam."

Ango Abdullahi ya kara da cewa, "a halin yanzu muna ganin yawaitar rashawa kuma babu wanda yake komai a kan hakan".

Ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata a garin Kaduna, jim kadan bayan bikin bude wani taro mai take, "Ilimi a matsayin hanyar hadin kan kasa. Rikice-rikicen arewacin Najeriya."

Kamar yadda dattijon ya ce, idan har Shugaban kasa Buhari ya shirya yaki da rashawa, kotu da gidajen gyaran hali na kasar nan, da yanzu sun cika da 'yan siyasa masu sama da fadi da kudin jama'a.

DUBA WANNAN: Shan sigari a cikin jirgi: Kotu ta yanke wa fasinja hukuncin zaman gidan yari da tara

Ya ce akwai 'yan siyasa masu yawa da ke yawonsu hankali kwance saboda APC ta yafe musu zunubbansu. Ya kafa misali da abinda ya gifto zuciyarsa a lokacin na yadda aka yafe wa Sanata Danjuma Goje zunubbansa saboda ya koma APC, kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito.

Ya ce, "Shugaban kasa ya ce yana yaki da rashawa amma ban amince da hakan ba, idan da hakan gaskiya ne da tuni kotu da gidajen yarin kasar nan na cike a halin yanzu. Hakan zai faru ne saboda akwai rashawa a ko ina."

"Ba a daukar matsala daya kacal a mayar da ita misali na yaki da rashawa. Mun ga yadda aka yankewa Uzor Kalu hukunci kuma duniya ta san da hakan. Amma akwai mutane da ke rike da biliyan saba'in da doriya a tare dasu. Wadannan mutanen suma ya kamata a ce suna tare da Uzor Kalu ne." cewar dattijon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel