Ganduje ya gwangwaje Sadiq Daba ta kyautar miliyan N1

Ganduje ya gwangwaje Sadiq Daba ta kyautar miliyan N1

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alkawarin bayar da tallafin kudi, miliyan N1, ga tsohon jarumi kuma mai gabatar da shiri, Sadiq Daba.

Ganduje ya dauki alkawarin ne ranar Asabar, 14 ga watan Disamba, yayin taron bayar da kyauta ga jaruman masana'antar Nollywood, wanad aka yi a dakin taro na 'Coronation' da ke fadar gwamnatin jihar Kano.

Masu shirya taron sun gabatar da nasarorin da jarumin ya samu yayin da yake kan ganiyarsa kafin Ganduje ya gabatar da kyautar gare shi.

Ganduje ya gwangwaje Sadiq Daba ta kyautar miliyan N1
Ganduje da Sadiq Daba da jaruman Nollywood
Source: Facebook

Gwamnan ya bayar da gudunmawar ga jarumin ne a matsayin tallafi ga neman taimakon neman lafiyarsa.

DUBA WANNAN: Kano: Kotu ta jaddada karfin ikon Ganduje na tumbuke sarakunan jihar

Yayin bikin bayar da kyautar, Daba ya bayyana cewa shi dan asalin jihar Kano ne amma kuma yana zaune ne a garin Jos, jihar Filato.

Tallafin na gwamna Ganduje yana zuwa ne makonni biyu bayan Dakta Joe Okei Odumakin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tallafa da kudi domin ceto rayuwar jarumin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel