Rundunar mayakan sama sun yi ragargaza gidan ajiyan yan ta'addan ISWAP

Rundunar mayakan sama sun yi ragargaza gidan ajiyan yan ta'addan ISWAP

Hukumar mayakan saman Najeriya ta ce jami'anta sun ragargaza wajen ajiyan kayayyakin yan ta'addan daular Musulunci a yankin Afrika ta yamma dake Kirta Wulgo, yankin tafkin Chadi dake Arewacin Borno.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Air Komodo, Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan ne a hawabin da ya saki ranar Talata a Abuja.

Yace: "An kai harin ne sakamakon rahoton cinne da muka samu cewa yan ta'addan ISWAP suna amfani da wasu gidajen uku masu rufin ruwan ganye wajen ajiye kayan abinci, kayyayakin motoci, jiragen ruwa da sauransu."

Daramola ya ce hukumar, za ta cigaba da namijin kokarin da takeyi har sai ta share da yan ta'adda daga yankin Arewa maso gabas.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel