Shan sigari a cikin jirgi: Kotu ta yanke wa fasinja hukuncin zaman gidan yari da tara

Shan sigari a cikin jirgi: Kotu ta yanke wa fasinja hukuncin zaman gidan yari da tara

A jirgin kamfanin Air Peace mai lamba P4 7558 ne wanda ya taso daga Sharjah zuwa Legas aka kama wani fasinja da laifin shan sigari a cikin jirgin.

Bayan kama fasinjan ne aka mikasa ga jami'an tsaro inda babu dadewa aka gurfanar da shi gaban kuliya.

Kotun majistare da ke Ogba ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na makonni biyu tare da cin tararsa har N200,000.

Wani ma'aikacin jirgin ne Adewale Oyebade ya kama fasinjan yana shan sigari a yayin da jirgin ke sararin samaniya a ranar 11 ga watan Disamba, 2019.

Sau da yawa, ma'aikatan cikin jirgin kan sanar da fasinjoji cewa ba a amfani da hayaki a lokacin da jirgin ya daga.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta yi kiran gaggawa ga Malami da shugaban hukumar DSS

Kamar yadda shugaban fannin sadarwa na kamfanin jiragen sama na Air Peace, Stanley Olisa ya sanar, ya ce fasinjan ya karya dokar hana shan sigari a jirgi. Ya tabbatar da cewa, dole ne a jinjinawa kokarin Oyebade ta yadda ya tabbatar da tsaro a jirgin. Bankado fassinjan da ke shan sigari a jirgin abun a yaba masa ne.

Ya kara da cewa, Oyebade ya gano fasinjan na aikata haramtaccen abun ne a yayin da yake kokarin sauke nauyin aikinsa da yake.

A mayar da martanin kamfanin jirgin saman: "Muna da matukar mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron fasinjojinmu kuma ba zamu sassauta hakan ba ko kadan."

Olisa ya jinjinawa kotun ta yadda ta hanzarta yanke hukunci, ya kara mika godiya ga fasinjojin da ke amfani da jiragensu tare da tabbatar musu da cewa tsaro ne kan gaba a harkar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel