Ba ni da lafiya, ina bukatan ganin likitan gargajiya - Orji Uzor Kalu ya nemi kotu ta basa beli

Ba ni da lafiya, ina bukatan ganin likitan gargajiya - Orji Uzor Kalu ya nemi kotu ta basa beli

- Orji Uzor Kalu ya sake magana daga gidan gyara hali

- Wannan karo, Sanatan ya bukaci kotu ta sake bashi beli domin ya je ganin bokansa

- Kalu ya bayyana cewa bashi da lafiya kuma ba zai iya samun isasshen kula daga asibitin dake cikin kurkukun ba

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, wanda babbar kotun tarayya dake Legas ta yankewa hukuncin shekaru 12 a gidan yari ya bukaci kotu ta sake bashi beli a yau Talata, 17 ga Disamba, 2019.

Kalu ya bayyanawa kotu cewa yana bukatan belin ne saboda yana fama da rashin lafiya kuma ba zai iya samun isasshen kula daga asibitin dake cikin kurkukun ba, saboda haka yana bukatar bokansa.

Hakazalika, ya bayyanawa kotu cewa mazabarsa da yake wakilta a majalisar dattawa za tayi rashi babba idan ya cigaba da kasancewa cikin kurkuku. The Nation ta ruwaito.

Amma bukatar Kalu ta samu cikas inda lauyan hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ya nuna rashin amincewarsa.

Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs SAN, yace babu wani takardan asibiti mai sa hannun likita da ya nuna cewa Kalu na fama da rashin lafiya, kuma takardan da ya gabatar, tsohuwa ce.

Jacob ya kara da cewa bukatar Kalu na son ganin likitan gargajiya ba zai yiwu ba, tunda ana bari baki su kawo masa ziyara, saboda haka shi ma yazo.

Alkali mai shari'a ya dage karar zuwa ranar 23 ga Disamba, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel