Sanatoci ba su amince a rika bada biza nan-take ga ‘Yan kasashen Afrika ba

Sanatoci ba su amince a rika bada biza nan-take ga ‘Yan kasashen Afrika ba

Mun ji cewa Majalisar dattawan ba ta yarda da batun bada takardun biza nan-take da zarar ‘Yan kasashen Afrika sun shiga cikin Najeriya. ‘Yan majalisar sun nuna ba su tare da wannan tsari.

Kwanakin baya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa gwamnatin Najeriya za ta rika bada takardun shiga kasa ba tare da wata-wata ba ga duk mutanen da ke Nahiyar Afrika.

A zaman da Majalisar dattawa ta yi a farkon makon nan, wasu Sanatoci sun fito sun nuna rashin goyon bayansu a game da wannan. Wannan ya sa majalisar ta ce za ta gayyaci Ministan gida.

Sanata Abba Moro mai wakiltar Yankin Benueai ya bayyana cewa akwai bukatar majalisa ta sa baki kafin gwamnati ta dauki mataki game da sha’anin bada takardun shigowa cikin Najeriya.

KU KARANTA: Kasafin kudin 2020 ya shiga cikin doka a Najeriya

Sanatocin sun ci ma matsayar cewa za su kira Ministan harkokin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da shugaban hukumar maganin fasa-kauri, Hameed Ali, domin su yi masu kwakkwaran bayani.

Wadannan manyan jami’an gwamnatin za su zauna ne a gaban kwamitin harkokin cikin gida da na shari’a domin su ji dalilin da ya sa gwamnatin Buhari za ta rika bada biza ga kowa daga 2020.

“Za a aika masu gayyatar ne domin su yi wa Sanatoci bayanin hurumi da tsare-tsare da abin da tsarin mulki ya ce kafin soma bada takardun shiga kasa nan-take ga masu ziyartar Najeriya.”

Sanata Adewunmi Adetunbi da Barau Jibrin sun nuna goyon bayansu ga wannan tsari da a cewarsu ake yayi a Duniya, yayin da irinsu Eyinnaya Abaribe su ke ganin hakan na da hadari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel