Ya kamata Adams Oshiomhole ya yi murabus – Inji Edo APC

Ya kamata Adams Oshiomhole ya yi murabus – Inji Edo APC

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust cewa Jam’iyyar APC ta reshen jihar Edo, ta na so shugaban jam’iyya na kasa baki daya, Adams Oshiomhole ya sauka daga kan kujerarsa.

Shugaban APC na jihar Edo, Anselm Ojezua, ya zargi tsohon gwamnansa Adams Oshiomhole da rasa wasu dabi’un da ake bukata wajen wanda zai rike shugabancin jam’iyyar mai mulki.

A cewarsa, Kwamred Adams Oshiomhole, bai da dattaku da damar da zai cigaba da jan ragamar ‘Ya ‘yan jam’iyyar. Anselm Ojezua, ya yi wannan jawabi ne a Sakatariyar APC ta Edo.

Mista Anselm Ojezua ya nemi shugaban jam’iyyar na APC na-kasa ya sauka daga kan kujerar da ya ke kai ne tun da an dakatar da shi a matsayin ‘Dan jam’iyya a Gundumar Mazabarsa.

KU KARANTA: Kotu ta ba Gwamna Ganduje damar tunbuke Sarakunan Kano

Ya kamata Adams Oshiomhole ya yi murabus – Inji Edo APC

An taso Adams Oshiomhole ya sauka daga kujerar Shugaban Jam’iyya daga gida
Source: Twitter

Shugaban jam’iyyar na reshen Edo, ya kuma zargi Oshiomhole da jawo rigimar da aka shiga a jihar Edo da nufin batawa gwamna Godwin Obaseki da shugabannin APC na jihar suna.

Ojezua ya ke cewa Adams Oshiomhole wanda ya sauka daga gwamna a 2016 ya kitsa rikicin da ya barke a jihar Edo ne saboda ya canza shugabannin da ke mulkin jihar da karfi da yaji.

Da ya ke maida martani a madadin bangaren shugaban APC na kasa, Mista Lawrence Okha, ya yi watsi da kiran da shugaban jam’iyyar na gida ya ke yi wa Adams Oshiomhole ya sauka.

Lawrence Okha ya bayyana cewa ‘Yan kungiyar tafiyar gwamna Obaseki da mataimakinsa, Shuiabu ne su ka fito su na wannan magana ba wai ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC na halal ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel