Kebbi da Jigawa ne kashin-baya a game da rashin kwararrun Malaman Makaranta

Kebbi da Jigawa ne kashin-baya a game da rashin kwararrun Malaman Makaranta

Wani bincike da hukumar da ke binciken ma’aikatan Najeriya ta yi, ya nuna cewa Malaman makarantun gwamnati da ba su kware sosai a wajen aiki ba sun fi yawa a wasu jihohin Arewa.

Jihohin Kebbi, Legas da Jigawa ne su ka zo kan gaba a wannan sahu na jihohin da ake fama da Malaman da ba su da nagarta. An fito da rahoton binciken ne a dakin taro na ICC da ke Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da rahoton wannan muhimmin bincike da aka yi. Ministan ilmi, Adamu Adamu, shi ne ya wakilci Mai girma shugaban kasar a wajen taron.

Binciken ya nuna cewa a yanzu haka akwai gibin kwararrun Malamai 277, 537 da ake nema a kasar domin bunkasa harkar ilmi. Kwararren Malami shi ne wanda ya ke da akalla shaidar NCE.

KU KARANTA: Kasafin Gwamnatin Buhari na sama da Tiriliyan 10 zai zama doka

Jaridar Daily Trust ta cewa hakan na zuwa ne bayan an ji cewa UBEC ta kashewa jihohin Naira biliyoyin kudi ta hannun hukumar UBEC domin inganta ilmi, wanda ya ke cikin wani irin hali.

Jihohin da su ke tsananin fama da rashin isassun malaman da su ka dace su shiga aji su ne: Kebbi, Legas, Jigawa, Gombe, Zamfara da Imo. Jihohin Arewa biyu ne su ka shiga sahun farko.

Oyo ce jihar ta fi kowace yawan kwararrun Malamai a fadin kasar. A game da yawan Malamai a makarantun gwamnati; Kano ce gaba, sannan Legas, sai Kaduna, sai Neja. Bayelsa ce a karshe.

An kuma gano cewa an fi samun kwararrun Malamai a makarantun gwamnati fiye da makarantun kasuwa. Minista Adamu Adamu, ya yi jawabi a madadin shugaban kasa a taron.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel