APC: Ku fito ku yi wa ‘Yan Najeriya bayani kan zargin badakalar FIRS – PDP

APC: Ku fito ku yi wa ‘Yan Najeriya bayani kan zargin badakalar FIRS – PDP

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga APC mai mulki ta yi wa Duniya bayani mai gamsarwa game da yadda ta karkatar da Naira biliyan 40 wajen zaben 2019 daga harajin da jama’a su ka biya.

Babbar jam’iyyar hamayyar ta zargi APC da salwantar da kudin da ke cikin asusun hukumar FIRS domin yakin neman zabe. PDP ta yi wannan jawabi ne ta bakin Kola Ologbondiyan jiya a Abuja.

Da ya ke jawabin a Ranar 16 ga Watan Disamba, 2019, Mista Kola Ologbondiyan, ya ce zargin da ke yawo a Najeriya na wawurar kudi a FIRS ya fara tadawa fadar shugaban kasa Buhari hankali.

PDP ta ce: “Rahotannin da su ka karada gari ya nuna cewa APC ba ta da tausayi, kuma jam’iyya ce mai kala biyu, wanda ta ke jin dadin sace dukiyar kasar da ya kamata jama’armu su amfana.”

KU KARANTA: Buhari ya sa hannu a kundin kasafin kudin shekara mai zuwa

Malam Lanre Issa-Onilu, ya maida martani ta bakin Takwaran Kola Ologbondiyan, inda ya karyata zargin. Jam'iyyar APC ta kalubalanci PDP ta kawo hujjojin zargin cin kudin gwamnati.

“Rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yada labarai da jawabi daga bakin PDP cewa hukumar tattara harajin FIRS ta ba APC domin yakin neman zaben 2019, zargin kanzon-kurege ne.”

APC ta kira wannan magana da zargi maras tushe. "Babu basira a cikin wannan zargi na mummmunan yunkurin bata suna. Babu wanda ya yarda da labarin, sai wanda su ka wallafa shi.”

Mu na kira ga masu yada wannan labari su tsaya a wuri guda, a baya sun ce Biliyan 90, yanzu sun ce Biliyan 40. Mu na kalubalanta su kawo shaidar wata hukuma ta ba APC kudin yakin zabe.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel