Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 na kudi N10.59 trillion a yau Talata, 17 ga watan Disamba, 2019.

Shugaban kasan ya rattafa hannunsa kan kasafin kudin ne tare da mataimakinsa, Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila.

Hakazalika akwai shugaban kwamitin kasafin kudi, Sanata Barau Jibrin; ministar kudi, Zainab Ahmad Shamsuna; ministan kasafin kudi, Jedi Agba da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020
Source: Facebook

A ranar 13 ga watan Disamba, majalisar dokokin tarayya ta aikawa shugaba Muhammadu Buhari da kasafin kudin inda fadar shugaban kasa tace shugaba Buhari da majalisar zantarwa zasu zauna domin dubi cikin takardar.

A ranar 5 ga Disamba, 2019, Yan majalisan sun tabbatar da kasafin kudin ne bayan kimanin kwanaki arba'in da shugaban kasa ya gabatar da takardan gabansu.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya kawo kasafin majalisa bayan kwamitinsa ta kammala bincikenta.

Yan majalisun sun kara kudin da Buhari ya gabatar daga N10.33 trillion zuwa N10.6 trillion (10,594,362,364,830).

Ga kiyasin da aka gina kasafin kudin kai da hotunan taron:

Danyen man da za'a rika haka a rana: Ganga milyan 2.18

Farashin kowani Ganga daya a : $57

Farashin Dala: N305 / $

Kudin shigan da ake sa ran samu a shekerar 2020:

Dagar arzikin Man fetur : 2.64 trillion

Arzikin Sabanin Mai (Haraji) : 1.81 trillion

Sauran hanyoyi ( sauransu) : 3.7 Trillion

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel