Buhari ya gargadi yan siyasa: Kada wanda ya saka ni a cikin sabgar siyasar a 2023

Buhari ya gargadi yan siyasa: Kada wanda ya saka ni a cikin sabgar siyasar a 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan siyasar Najeriya, musamman masu burin tsayawa takara ko wacce iri a zaben shekarar 2023 dasu kada su kuskura su sanya shi cikin sabgar siyasarsu.

Daily Nigerian ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 17 ga watan Disamba yayin da yake tarbar manyan baki da suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock Villa domin taya shi murnar cika shekaru 77 a duniya.

KU KARANTA: Cika shekaru 77: Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Buhari ya nemi yan siyasa masu burin tsayawa takara a zaben 2023 da su kasance sun yi aiki tukuru wajen yakin neman zabe, domin kuwa a wannan karo ba zai sake bari a yi amfani da sunansa wajen tafka magudin zabe ba.

Haka zalika shugaban kasa ya gargadi duk masu kokarin yin amfani da hukumomin tsaro da jami’ansu wajen gudanar da magudin zabe a zaben 2023 da cewa sun makara, kuma su sake tunani, domin ba zai taba bari su cika wannan buri nasu ba.

“Alkawarin da nake son yi ma yan Najeriya shi ne zan yi aiki tukuru don ganin an gudanar da zaben gaskiya da gaskiya. Duk masu son shiga majalisar dokoki da fadar shugaban kasa dole ne su dage su aiki tukuru, saboda zan yi amfani da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaben gaskiya da gaskiya.

“Ba zan bari wani ya yi amfani da ofishinsa, mukaminsa ko kudinsa wajen tilasta kansa a kan yan Najeriya ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, kafatanin gwamnonin yankin nahiyar Arewacin Najeriya sun taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da cika shekaru 77 a duniya a ranar Talata, 17 ga watan Disamba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar inda ya jinjina ma Buhari bisa halinsa na dattaku, rikon amana, kishin kasa da kyakkyawan salon mulki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel