Yanzu-yanzu: Kotu ta yi kiran gaggawa ga Malami da shugaban hukumar DSS

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi kiran gaggawa ga Malami da shugaban hukumar DSS

Wata babbar tarayya da ke Abuja ta yi kiran gaggawa ga ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami da kuma shugaban hukumar jami'an tsaron fararen kaya, Yusuf Bichi a kan kara damke Omoyele Sowore.

Kotun ta bukacesu ne da su gurfana a gabanta a ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, sakamakon garkame Omoyele Sowore da suka yi ba bisa ka'ida ba.

Jastis Inyang Ekwo ya bada wannan umarnin ne a ranar Litinin, bayan bukatar da Marshal Abubakar, shugaban kungiyar lauyoyin Sowore ya mika gaban kotun ta sakin wanda yake karewa.

Idan zamu tuna, a ranar Litinin ne ministan shari'ar Najeriya din, Abubakar malami ya sanar da cewa, bashi da hurumin yanke hukunci ko kuma mika bukatar sakin Omoyele Sowore daga hannun jami'an tsaron fararen kaya.

DUBA WANNAN: Laifin kisan kai: Kotu ta yankewa dan wani babban basarake hukuncin kisa

Idan zamu tuan, bayan kasa da sa'o'i 24 da sakin jagaban #RevolutionNow, Omoyele Sowore daga hannun jami'an tsaron faraen kaya, sun kara cafkesa bayan da aka kammala zaman kotu.

Wannan lamarin kuwa ya jawo wani 'matsakaicin wasan kwaikwayo' a cikin dakin kotun.

Duk da kuwa, hukumar DSS din ta musanta kama Sowore a cikin kotu, ta tabbatar da cewa fitowar Sowore daga kotun kenan ya ci karo dasu. Lamarin da ya jawo Sowore ya runtuma a guje ya fada dakin kotun.

Hakan kuwa ya jawo cece-kuce daga mutane da kungiyoyi daban-daban. A hakan ne kuwa hukumar jami'an tsaron ta fararen kayan suka cigaba da tsare Sowore din har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel