Yanzu-yanzu: Dokar mayar da wa'adin shugaban kasa da yan majalisa zuwa daya mai shekaru 6 ya samu koma baya

Yanzu-yanzu: Dokar mayar da wa'adin shugaban kasa da yan majalisa zuwa daya mai shekaru 6 ya samu koma baya

Kokarin kawo sauye-sauye cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ya samu koma baya a majalisar wakilan tarayya ta tara.

A ranar Talata, 17 ga watan Disamba, yan majalisar wakilan tarayya sun ki amincewa da takardar dokar canza wa'adin kujeran shugaban kasa daga guda biyu na shekaru hudu-hudu zuwa wa'adi daya mai shekara shida a jere.

Hakazalika, yan majalisar sun bukaci a sauya wa'adin yan majalisu daga shekaru hudu-hudu zuwa wa'adi daya mai shekaru shida.

Dokar ta samu koma baya yayinda yan majalisan suka hanata tsallake mataki na biyu.

Yawancin yan majalisan sun ce yan Najeriya za su yi musu mumunan zato idan suka amince da dokar.

Dan majalisa daga jihar Benue, John Dyegh, ne ya kawo kudirin majalisa.

A wani labarin daban, shugaba Muhammadu Buhari zai samu biyan bukatarsa yayinda shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa majalisar zata baiwa shugaban kasa daman karban bashin $29.96 billion.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai a Abuja.

A cewarsa, majalisar zata sa ido kan yadda za'a kashe kudin idan an karbo.

Za ku tuna cewa majalisar dattawa karkashin tsohon shugabanta, Bukola Saraki, ta hana Buhari karbo bashin a shekarar 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel