Ba zan fifita wani dan siyasa kan wani a zaben 2023 ba - Buhari

Ba zan fifita wani dan siyasa kan wani a zaben 2023 ba - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai fifita wani dan siyasa domin ya daburta zaben 2023 ba, kuma yayiwa yan Najeriya alkawarin zabe cikin zaman lafiya da lumana.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ya fadi hakan ne da safiyar Litinin inda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da wasu hadiman Buhari suka shirya bikin tayashi murnan cikansa shekaru 77 da haihuwa a fadar shugaban kasa Abuja.

Shugaban kasan ya baiwa yan siyasan da ke da niyyar takara a zaben 2023 shawarar cewa su fara aiki domin al'umma su amince da su saboda ba zai fifita wani dan siyasa ko kakabawa yan Najeriya wani ba.

Hakazalika ya yi kira ga mambobin jam'iyyarsa, suyi aiki tukuru saboda ba zai amince wani yayi amfani da sunansa wajen yakin neman zabe ba.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 na kudi N10.59 trillion a yau Talata, 17 ga watan Disamba, 2019.

Shugaban kasan ya rattafa hannunsa kan kasafin kudin ne tare da mataimakinsa, Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila.

Hakazalika akwai shugaban kwamitin kasafin kudi, Sanata Barau Jibrin; ministar kudi, Zainab Ahmad Shamsuna; ministan kasafin kudi, Jedi Agba da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel