Kano: Kotu ta jaddada karfin ikon Ganduje na tumbuke sarakunan jihar

Kano: Kotu ta jaddada karfin ikon Ganduje na tumbuke sarakunan jihar

- A yau ne alkalin babbar kotun jihar Kano ta jaddada karfin ikon Gwamna Ganduje na tumbuke rawani sarakunan jihar Kano

- Da farko dai, kotun ta dakatar da wannan hukuncin ne sakamakon karar da majalisar nada sarakunan jihar ta shigar

- Majalisar nadin sarkunan jihar ta shigar da kara ta hannun lauyanta inda ta bukaci kotun ta dakatar da gwamnan daga tabbatar da sabbin dokokin masarauta ta 2019

A yau Talata ne Jastis A. T Badamasi na babbar kotun jihar Kano, ya dage hukuncin da ke hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje karfin iko a kan majalisar masarautar Kano.

Lauyan majalisar nadin sarakunan, a karar da suka shigar mai lamba K/197/2019, ya roki kotun da ya dakatar da karfin ikon Gwamna Ganduje har zuwa lokacin da shari’a makamanciyar wannan zata kammala.

DUBA WANNAN: Abubuwa 11 da yakamata a sani game da Shugaba Buhari yayin cikarsa shekaru 77

A hukuncin da kotu ta yanke a yau, kotu ta jaddada karfin ikon gwamnan wajen tumbukewa ko tsige sarakunan jihar kamar yadda sabbin dokokin masarautar jihar Kano din na 2019 suka tanada.

Wannan karfin ikon kuwa ya kunshi sauke rawanin kowanne Sarki da ya nemi takawa ko yin karantsaye ga sabbin dokokin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel