EFCC na binciken gwamnatin tsohon gwamna AbdulAziz Yari kan badakalar N200bn

EFCC na binciken gwamnatin tsohon gwamna AbdulAziz Yari kan badakalar N200bn

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bayyana cewa tana binciken sama da lamura 60 na almundahanar N200bn karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari.

Shugaban hukumar sashen yankin, Abdullahi Lawal, ya bayyana hakan ne a jihar Sokoto inda yake mikawa sakataren gwamnatin jihar Zamfara kekunan a daidaita sahu 53 da aka kwato hannun wani dan kwangila.

Abdullahi Lawal ne shugaban hukumar na jihar Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Lawal ya ce wadanda suka shigo da kararrakin sun hada da ma'aikatan gwamnati, ma'aikatu da kamfanoni masu zaman kansu.

A cewarsa, hukumar EFCC ta daskare asusun bankin dukkan wadanda ke da kashi a gindi.

Yace:"Kamar yadda kuka sani, hukumar na gudanar da bincike kan ayyukan gwamnatin da ta shude kuma muna tabbatarwa al'ummar jihar Zamfara cewa hukumar ba zatayi kasa a gwiwa ba wajen hukunta wadanda aka kama."

A bangaren gwamnatin jihar kuwa, Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Umaru, ya ce hujjoji sun bayyana yadda akayi badakalar sama da bilyan dari biyu.

Yace: "Mun kwato biliyoyi kuma har yanzu muna sauraron wasu. Amma bisa ga kararrakin da aka kawowa gwamnatin jihar, kimanin tiriliyan biyu ne."

"Lallai wadannan kudaden zasu taimakawa gwamnatin jihar wajen yaki da talauci da kuma karfafa tattalin arzikinta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel