EFCC ta kwato 'a daidaita sahu' 53 da aka karkatar lokacin AbdulAziz Yari

EFCC ta kwato 'a daidaita sahu' 53 da aka karkatar lokacin AbdulAziz Yari

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta kwato kekunan 'a daidaita sahu' 53 mallakan gwamnatin jihar Zamfara da aka karkatar lokacin tsohon gwamna AbdulAziz Yari.

Shugaban hukumar EFCC, sashen jihar Zamfara, Abdullahi Lawal, ya mika kekunan da aka kwato ga gwamnatin jihar.

A jawabin da ya gabatar lokacin da yake mika kekunan, Lawal ya bayyana cewa kekunan na cikin irinsu guda 1000 da gwamnatin ta siya N1.2 billion daga kamfanin Kymco and Wadatto Limited.

A cewar EFCC, dan kwangilan da tsohon gwamna AbdulAziz Yari, ya baiwa aikin ya ki kawo kekuna 53 bayan karewar wa'adin gwamnatin.

Lawal yace: "Kamar yadda kuka sani, hukumar na gudanar da bincike kan ayyukan gwamnatin da ta shude kuma muna tabbatarwa al'ummar jihar Zamfara cewa hukumar ba zatayi kasa a gwiwa ba wajen hukunta wadanda aka kama."

Yayinda yake karbar kekunan madadin gwamnatin jihar, sakataren gwamnatin jihar, Bala Umaru, ya mika godiyarsa ga hukumar EFCC.

Bala ya bada tabbacin cewa za'a raba kekunan ya jama'a bisa gaskiya da kuma luran hukumar EFCC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel