Abubuwa 11 da yakamata a sani game da Shugaba Buhari yayin cikarsa shekaru 77

Abubuwa 11 da yakamata a sani game da Shugaba Buhari yayin cikarsa shekaru 77

‘Yan Najeriya da yawa na ta tururuwar taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa a karo na 77 a yau ranar Talata, 17 ga watan Disamba.

A matsayinsa na tsohon shugaban kasa a mulkin soji kuma shugaban kasar Najeriya a halin yanzu, Buhari na da kyakyawan suna a tarihin kasar nan ta Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta tattara wasu abubuwa 11 game da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yakamata a sani a ranar zagoyawar haihuwarsa karo na 77.

1. An haifi Muhammadu Buhari ne a ranar 17 ga watan Disamba, 1942 a Daura. Sunan mahaifinsa Hardo Adamu, basaraken Fulani ne inda mahaifiyarsa sunanta Zulaihat.

2. Buhari ne ‘da na 23 a wajen mahaifinsa. Mahaifiyarsa ce ta raineshi bayan rasuwar Hardo Adamu a lokacin da Buhari yake da shekaru 4 kacal a duniya.

3. Buhari ya samu ilimi mai tarin yawa a Katsina, ya samu horon zama soja a Kaduna, Birtaniya, Indiya da Amurka.

DUBA WANNAN: Allahu Akbar: Wata yarinya mai shekaru 6 ta haddace Qur'ani a UAE

4. Yana daga cikin mashiryan juyin mulkin kwace mulkin Najeriya daga hannun janar Gowon a 1975, kuma an nada shi a matsayin gwamnan jihar Arewa maso Gabas ( jihar Barno a yanzu) a lokacin.

5. Janar Olusegun Obasanjo ya zabesa a matsayin kwamishinan albarkatun man fetur.

6. A shekarar 1977 Buhari ya zama sakataren soji a hedkwatar koli ta soji, wannan ne kuwa babbar kujerar gwamnati.

7. Buhari ya auri Aisha Halilu tun a shekarar 1789. A tare suka raini yara 5 da jika daya. Duk da yana da yara 5 daga aurensa na farko da marigayiya Safinatu Yusuf.

8. A 2003, Buhari ya nemi shugabancin Najeriya amma Olusegun Obasanjo ya kada shi a karkashin jam’iyyar PDP.

9. Buhari ya sake neman kujerar shugabancin kasa a 2007, inda marigayi Umaru Yar’adu ya kada shi.

10. A 2007, ya sake neman kujerar shugabancin kasa amma Goodluck Jonathan ya sake kada shi.

11. A 2014, jam’iyyar maja ta APC ta tsayar da Buhari a matsayin dan takararta inda a 2015 ya lashe zaben bayan ya kada shugaban kasa Goodluck Jonathan na wannan lokacin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel